NARD ta dakatar da shirin tafiya yajin aiki bayan shiga tsakani da masu ruwa da tsaki

Doctors NARD 750x430 (2)

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa NARD ta sanar da dakatar da shirin komawa yajin aikin da ba shi da iyaka kuma cikakke, wanda ta tsara farawa, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a matakin ƙasa.

Babban sakataren ƙungiyar, Dakta Shuaibu Ibrahim, ya tabbatar da matakin dakatarwar bayan taron gaggawa na kwamitin zartarwa na ƙasa na ƙungiyar da aka gudanar ta kafar sadarwa.

Ya bayyana cewa an yanke shawarar ne domin duba matsayin buƙatun ƙungiyar da kuma tantance irin ci gaban da aka samu ta hanyar tattaunawa da hukumomin gwamnati.

Ya ce dakatarwar ta kasance ta dabara kuma mai sharaɗi, domin bai wa ƙungiyar damar yin cikakken nazari kan ainihin ci gaban da aka samu a taron kwamitin zartarwa na ƙasa na gaba.

Ya ƙara da cewa kwamitin ya amince baki ɗaya da dakatar da yajin aikin bayan samun tabbacin aiwatar da matakai daga ma’aikatun lafiya da walwalar jama’a, kwadago da kuɗi.

Karanta: Likitoci za su koma yajin aiki mako mai zuwa

Sauran masu ruwa da tsaki da aka yi hulɗa da su sun haɗa da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati, ofishin babban akanta na ƙasa, tsarin biyan albashi na ƙasa IPPIS, ofishin kasafi, kwamitocin daraktocin manyan asibitoci, hukumar tsaron farin kaya, majalisar dokoki ta ƙasa da kuma mataimakin shugaban ƙasa.

Wannan ya nuna cewa an samu waɗannan tabbaci ne sakamakon tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa a madadin shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Dangane da buƙatun ƙungiyar, an bayyana cewa kwamitin da ke kula da rikicin asibitin koyarwa na tarayya da ke Lokoja ya aiwatar da shawarwarin da aka bayar, tare da kafa kwamitin sulhu domin samar da daidaito da zaman lafiya a wuraren aiki.

Haka kuma, an tura jerin sunayen bashin albashi na kaso ashirin da biyar da talatin da biyar zuwa IPPIS, yayin da ma’aikatar kwadago ta yi hulɗa da ma’aikatar kuɗi domin tabbatar da biyan su cikin gaggawa.

Haka ma an kuma samu ci gaba kan alawus na kayan aiki, inda aka bi irin wannan tsari na tura bayanai zuwa hukumomin da suka dace.

Haka nan, jerin bashin ƙarin girma da albashi an isar da su ga ma’aikatar kuɗi da ofishin kasafi domin ɗaukar matakin gaggawa.

Kazalika an an fitar da sanarwar alawus na ƙwarewa, kuma ana sa ran fara cikakken aiwatarwa tare da albashin wata, tare da haɗa bashin watanni goma sha takwas a cikin kasafin kuɗin shekarar.

Ƙungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da matsa lamba domin ganin an kammala tattaunawar yarjejeniyar ta bai ɗaya ga dukkan likitoci cikin gaggawa.

A baya dai, ƙungiyar ta sanar da shirin komawa yajin aiki sakamakon matsalolin walwala, ƙarin girma, alawus da yanayin aiki, sai dai kotun masana’antu ta ƙasa da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na hana ɗaukar matakin yajin aiki, bayan shigar da ƙara daga babban lauyan gwamnatin tarayya da gwamnatin tarayya domin tabbatar da bin dokokin ƙwadago.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here