Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi domin halartar taron ci gaba mai dorewa

G aaC 9bgAAPQ24 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week na shekarar 2026, taron da ke haɗa shugabannin duniya kan batutuwan dorewar ci gaba.

Jirgin shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin sama na Zayed, inda Ministan ƙasa a ma’aikatar harkokin wajen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, ya tarbe shi a madadin gwamnatin ƙasar.

Ziyarar shugaban ƙasar zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta zo ne bisa gayyata a hukumance da daga Shugaban ƙasar, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyanya yi masa, a matsayin wani ɓangare na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Taron na shekara-shekara na zama dandali na duniya da ke haɗa shugabannin ƙasashe, ƙwararrun masana a fannonin masana’antu da ƙungiyoyin farar hula domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kirkire-kirkire a fannin makamashi da tsarin kuɗaɗe da ake buƙata wajen sauya sheƙa zuwa makamashin da ake sabuntawa.

A cewar bayanin da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan bayanai da dabaru ya fitar a baya, wannan ziyara na nuna ƙara ƙarfafa alaƙar Najeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, musamman a fannoni makamashin kore da haɗin gwiwar tattalin arziki.

Sanarwar ta bayyana cewa a yayin taron, Shugaba Tinubu na da niyyar gabatar da Najeriya a matsayin ƙasa mai taka rawa a fannin dorewar ci gaba, ta hanyar jawo jarin waje da samar da haɗin gwiwa da za su dace da manufofin bunƙasa ƙasar a matakin ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here