Dakarun Operation Hadin Kai sun fatattaki yan ta’addan ISWAP a Borno

ISWAP NEW 750x430

Dakarun Sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai OPHK, sun dakile wani gagarumin hari da ‘yan ta’addar ISWAP suka kai a garin New Marte na jihar Borno, inda suka yi nasarar kakkabe mahara da dama tare da kwato makamai da motoci har da ma da ababen fashewa, in ji rundunar sojin Najeriya a ranar Talata.

Harin da aka dakile ya faru ne da sanyin safiyar yau Talata 27 ga watan Mayu lokacin da ‘yan ta’addar suka yi yunkurin kutsawa wurin da sojojin suke.

An yi gumurzu bindiga tare da taimakon runduna ta 24 da Bataliya ta musamman ta 134 Inda suka yi gaggawar kai dauki don dakile harin.

Kaftin Reuben Kovangiya, mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin ta OPHK shi ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin na samun goyon bayan rundunar sojin sama ta Air Component wadda ke ba da bayanan sirri da kuma sa ido da kai hare-hare ta sama.

A cewarsa, harin da aka kai ta sama ya lalata babura da dama da maharan da ke tserewa ke amfani da su, yayin da sojojin kasa suka gano wata mota kirar Bama-bamai VBIED da ɓata gari suka gudu suka bar su lokacin da suke tserewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here