Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta dora laifin yawaitar jami’o’in dake bayar da digirin bugi a kan iyayen dalibai, saboda suke biyan kudi domin samun takardar digirin ga ya’yansu.
Mukaddashin sakataren zartarwa, Mista Chris Maiyaki, ne ya bayyana haka ranar Lahadi a Abuja yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).
Ya shaida wa NAN cewa jami’oin masu bayar da shaidar digiri tuni hukumar ta NUC ta haramtasu.
Maiyaki ya shawarci iyaye da su binciki jami’o’in sosai kafin su tura ya’yansu dakunan.