Samar da aikin yi: Daruruwan matasa sun yabawa dan majalisar tarayya a Kano

E7BFDE9E 3AA7 448F B9D3 AF5702F51B9B
E7BFDE9E 3AA7 448F B9D3 AF5702F51B9B

Daruruwan matasa daga kananan hukumomin Ungogo da Minjibir a jihar Kano sun yaba da wannan shiri da kokarin dan majalisar tarayya mai wakiltar yankunan a majalisar dokokin kasa, Hon. Sani Ma’aruf Mai Wake yayi domin samar da aikin yi ga matasa 133 da ba su da aikin yi.

Matasan sun bayyana jin dadinsu ne a karshen mako lokacin da suka karbi takardun samun aiki a wasu ma’aikatu da ha hukumomi na gwamnatin tarayya daban-daban.

Da yake jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Ibrahim Liti Dausayi ya yabawa dan majalisar, Sani Ma’aruf Mai Wake saboda irin yadda yake samawa al’ummar yankin aiki a gwamnatin tarayya.

“Muna matukar godiya da wannan damammaki mai kyau, zai taimaka matuka wajen rage radadin talauci a cikin al’ummarmu,” in ji Ibrahim Dausayi.

Tun da farko, Hon. Sani Ma’aruf Mai Wake, wakilin mazabar Ungogo da Minjibir a majalisar wakilai ta kasa, ya yi kira ga wadanda suka amfana da su kasance jakadu nagari na al’ummarsu.

Ya bukace su da su himmatu su ci gaba da nuna kyawawan halaye da aka san su da su.

Solacebase ta ruwaito cewa majalisar ya aza harsashin ginin makarantar Islamiyya da cibiya wanda ya ce za a kashe naira miliyan 87 tare da kayayyakin more rayuwa na zamani kafin kammalawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here