Ba’a kai hari mahaifar Boss Mustapha ba-Yan sanda

80500D47 67F4 4B7C 8999 357CB0B9F206
80500D47 67F4 4B7C 8999 357CB0B9F206

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta musanta rahoton da aka buga ta yanar gizo cewa ‘yan kungiyar Boko Haram da ‘yan bindiga sun kai hari a mahaifar sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce babu kanshin gaskiya a rahoton da ke cewa al’ummar kauyukan Dabna da Kwabre da ke gundumar Dagwaba a karamar hukumar Hong sun yi watsi da gidajensu sakamakon harin da ake zargin an kai musu.

Solacebase ta ba da rahoton cewa Sakataren Gwanatin tarayya daga wannan  yankin ya fito.

Nguroje ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa rundunar ‘yan sandan ta baza jami’an yaki da ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma jami’an tsaro a yankin.

Ya ce kawo yanzu babu wani rahoto daga jami’an tsaro cewa an kai hari a yankin.

Rundunar ta samu wasu bayanai da ba a tantance ba cewa mutane na gudun hijira daga wasu kauyuka sakamakon hare-haren da ake zargin Boko Haram da kai wa.

Shima da aka tuntubi Hakimin Dugwaba,  Simon Yakubu, ya yi watsi da rahoton ta yanar gizo tare da bayyana shi a matsayin “mai ruɗi”. Yakubu ya ce jama’a na zaune lafiya kuma suna bukukuwan Kirsimeti a kauyukan da aka ambata a cikin rahoton na yanar gizo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here