Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2022 a ranar Juma’a

EBD5A1C6 ED71 4C40 A036 933E88895980
EBD5A1C6 ED71 4C40 A036 933E88895980

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2022 a ranar Juma’a, kamar yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu, ne ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata a Abuja.

A cewarsa, majalisar ta mika kasafin kudin shekarar 2022 kuma shugaban kasar zai rattaba hannu kan dokar da karfe 10 na safe.

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da ‘yan majalisar wakilai a zauren majalisar wakilai da na majalisar dattawa suka amince da kasafin kudi na naira tiriliyan 17.126, wanda ya kara farashin  danyen mai daga dala 57 zuwa $62 kan kowacce ganga.

Gidan Talabijin na Channels ya samu wata sanarwa da magatakardan Majalisar, Mista Ojo Amos ya aike wa Fadar Shugaban Kasa.

Takardar mai lamba NASS/CNA/37/Vol.1/35 ta nuna cewa an mika kasafin ne a ranar Juma’ar da ta gabata kuma ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya karba a ranar Asabar.

Majalisar dattijai ta zartar da kasafin kudin shekarar 2022 a zamanta na ranar Larabar makon da ya gabata, inda shugaban majalisar, Ahmad Lawan, ya ba da tabbacin cewa za a aika da kudirin ga shugaban kasa domin ya rattaba hannu a washegari.

A nata bangaren, majalisar wakilai ta zartar da kasafin kudin a ranar Talatar da ta gabata. Majalisar ta kara daga jimillar kasafin kudin shekarar 2022 daga naira tiriliyan 16.391 zuwa naira tiriliyan 17.126.

Sanya hannu kan kasafin kudin kafin karshen shekara zai baiwa Najeriya damar ci gaba da tafiyar da tsarin kasafin na shekara guda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here