Tinubu ya amince da bada Naira biliyan 2 da shinkafa tirela 20 ga mutanen Mokwa

Floods Mokwa 750x430

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da fitar da kimanin Naira biliyan biyu da kuma shinkafa tirela 20 domin bai wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Niger.

Mataimakin shugaban Kashim Shettima, ne ya sanar da hakan ne a garin Mokwa, lokacin da ya kai ziyarar jaje kan ambaliyar ruwa da ta lalata tarin dukiya da kuma yin sanadiyyar salwantar rayukan mutane da dama.

Mataimakin shugaban ƙasan ya ce za a magance duk wasu matsaloli da ke addabar al’ummar jihar.

Haka kuma ya ce, shugaban Tinubu, ya bayar da umarnin gyara gadojin da ambaliyar ta lalata ba tare da ɓata lokaci ba.

Idan za a iya tunawa, dai hukumomi sun tabbatar da mutuwar sama da mutum 200 a ambaliyar ta ƙaramar hukumar Makwa da ke jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya.

Kana akwai fiye da mutum 500 da ba a san inda suke ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here