A kalla mutane 11 sun rasa rayukansu sanadiyyar wata wutar lantarki mai karfi da aka kawo a wasu yankunan birnin Zazzau dake Zaria a jihar Kaduna.
Yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Gwargwaje da Kauran Juli dake kan babban titin Kaduna zuwa Abuja.
“An kawo wata wutar lantarki mai karfin gaske a yankin ne misalin karfe 1:00 na dare. Hakan ya haifar da tartsatsi ta ko ina a mahadar wutar. Wanda yayi sanadiyyar konewar gidan wani Injiniya Zubair Abubakar yayin da sauran gidajen suka cigaba da fidda hayaki.”
Solacebase ta tattaro yadda wadanda suka rasa rayukansu suka hada da wata mata mai juna biyu, wata jami’ar kiwon lafiya, wani ‘dan sanda da sauran wasu da dama a yankin Gwargwaje.
Mrs Christy Lombo, matar ‘dan sandan da ya rasa ransa sanadiyyar gobarar lantarkin a barikin ‘yan sanda na Gwargwaje, ta bayyana yadda suke bacci lokacin da aka kawo wutar.
”Diyata ta tashi da dare, inda ta ga hayaki a wasu wurare a gidan. Hakan yasa ta tashe ni, sai dai kafin nan mijina ya riga ya tashi tare don ya kashe mahadar wutar gaba daya gidan. “Take yanke shokin ya kama shi gami da bugar dashi kasa saboda karfin wutar. Daga bisani muka garzaya dashi asibiti inda ya ce ga garinku.”
Kakakin hukumar wutar lantarki na Kaduna, Abdulazeez Abdullahi, a wata takarda da ya fitar ya ce binciken da aka yi ya bayyana cewa.
Lamarin ya auku ne sakamakon wuta mai karfi da aka kawo ta waya mara karfi, wacce tayi sanadin sakin wuta ba bisa ka’ida ba.
“An hanzarta bude hanyar shanye wutar cikin gaggawa don gudun cigaba da barna.
“Mun cigaba da lura da lamarin, sannan mun sanar da aukuwar mummunan lamari. Muna bayyana alhininmu da ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu bisa aukuwar lamarin.”
Haka zalika, hukumar ta jinjinawa Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, bisa gudunmawar da ya bada bayan aukuwar lamarin.













































