A ranar Alhamis ne Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Najeriya ta yi kira da a tattauna tsakanin gwamnatin tarayya da matasan da ke shirin fara zanga-zangar.
Oba Adeyeye Ogunwusi, Ooni na Ife kuma Mataimakin Shugaban Majalisar, ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar Shugaban kasa, bayan wata ganawa da Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce majalisar zartaswa ta tarayya ta yi wa sarakuna bayanin yadda ya kamata kan tsare-tsaren gwamnati da nasarorin da aka samu kawo yanzu, da kalubalen da ba a taba samu ba.
“Kamar yadda kuka sani, mun fi kusanci da mutane kuma mun san inda suke fuskantar kalubale.
Karin labari: Kotu ta tsaida ranar sauraren karar gwamnatin Edo da Shu’aibu
“Saboda haka, akwai hanyar da ta dace wajen dakile tabarbarewar harkokin mulki tsakanin masu mulki da kuma al’ummar da ke rike da mukaman gwamnati.
“Mutanen da suke can don yin zanga-zangar, hakkinsu ne na jama’a, amma su sanya ido a kai, kada su bari wasu da ke da wata manufa su sace shi. Wannan ita ce matsayarmu,” inji shi.
Ya ce sarakunan gargajiya ba za su kwadaitar da jama’a musamman matasa su rika yin satar dukiyar jama’a da kuma haddasa tabarbarewar doka da oda ba.
“Mu iyaye ne, mu sarakunan gargajiya ne, mun fi kusa da su, za mu koma gida mu ci gaba da wayar musu da kai” in ji Adeyeye.
Ya ce sarakunan gargajiya suna sane da kalubalen da ke fuskantar ‘yan Najeriya kamar yadda NAN, ta tabbatar.