Hukumar NYSC ta janye ‘yan bautar kasa daga makarantar Kwara saboda cin zarafi yar bautar kasa

Assaulted Corps member 608x430

Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) ta janye duk masu yi wa kasa hidima na da aka aika zuwa makarantar sakandare ta gwamnati da ke Kulende, Ilorin a jihar Kwara, biyo bayan duka da wata malamar makarantar ta yi wa wata ‘yar bautar kasa.

Rahotanni sun nuna cewa kimanin ‘yan NYSC mata 10 zuwa yanzu dake koyarwa a makarantar ne hukumar NYSC reshen jihar ta janye su daga makarantar domin tabbatar da tsaron lafiyarsu. Lamarin dai ya shafi wata mata ‘yar bautar kasa ne, wadda wata malama ta ci zarafinta bisa zargin rashin mutuntawa a makon jiya.

Babban Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Y.D. Ahmed, ya ziyarci makarantar a ranar Litinin din da ta gabata don magance matsalar kafin ya wuce sansanin horar da ‘yan bautar kasa na 2024 Batch C, Stream 2 Corps da ke Yikpata, karamar hukumar Edu ta jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here