Kotu ta bada belin Hadi Sirika da ‘yarsa da wasu mutum 2 kan kudi miliyan 100 ga kowannensu

Hadi sirika, kotu, beli, kudi, miliyan
A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika da diyarsa da wasu...

A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika da diyarsa da wasu mutane biyu kowannen su akan kudi miliyan 100.

Ana tuhumar su ne bisa zargin zamba har naira biliyan 2.7.

A cewar kotun, za su kuma bayar da wasu mutum biyu da za su tsaya masu da su ne suka mallaki kadarori a Abuja.

Karin labari: Ambaliya: Gwamna Namadi ya bada umarnin gina katangar ruwa a Jigawa

Kotun ta ce wadanda za su tsaya masa, dole ne su zama ‘yan kasa da ke da alhaki.

Waɗanda za a tabbatar sun kasance dole ne su gabatar da takaddun shaida.

Kotun ta kuma hana wadanda ake tuhuma fita kasashen waje ba tare da izininta ba.

Karin labari: Dalilin da yasa Gwamnan Kano ya cire shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar

Mai shari’a Oriji ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma a gidan yari idan har suka kasa cika sharuddan belinsu.

Za’a fara shari’ar ne a ranakun 10 da 11 da kuma 20 ga watan Yuni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here