Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya umarci ma’aikatar muhalli da ta gaggauta gina katanga a wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa domin duba matsalar ambaliyar ruwa a jihar.
Gwamnan ya ce matakin ya zama dole saboda damina ta shekarar 2024 ta gabato.
Babbar mataimakiyar gwamnan ta musamman kan harkokin yada labarai Hajiya Zainab Rabo ta bayyana matsayin Namadi a wata sanarwa da ta fitar a Dutse ranar Alhamis.
Karin labari: ASUU ta koka kan watsi da wasu bukatun Jami’ar Yusuf Maitama a Kano
Rabo ta ce gwamnan ya umarci kwamishinan muhalli na jihar, Dakta Nura Ibrahim da sauran jami’an ma’aikatar da su fara aikin a ranar Laraba.
Mai taimakawa gwamnan ta ce Namadi ma ya ba ma’aikatar muhalli izinin daukar wasu matakan gaggawa don tabbatar da ingantacciyar hanyar shawo kan ambaliyar ruwa a shekarar.
Karin labari: Dalilin da yasa Gwamnan Kano ya cire shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar
Ta ce matakan da suka hada da kawar da magudanar ruwa da kuma hana zubar da shara a magudanan ruwa, ya zama wajibi domin dakile matsalar ambaliyar ruwa a jihar.
A cewar ta, matakin da aka dauka zai kai ga kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.
Rabo ta ci gaba da ce an kafa kwamitin mutum tara da jihar ta kafa domin zagayawa da tallafawa al’umma kan nasarar aiwatar da wannan umarni kamar yadda jaridar NAN ta bayyana.