Babban bankin Najeriya (CBN) ya ayyana cewa tsoffin takardun naira da ya sauya N200, N500 da N1000 sun zama mara amfani tun ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023.
Jaridar solacebase ta tattaro cewa tun asali CBN ya zaɓi wa’adin 31 ga watan Janairu a matsayin ranar karshe ta ci gaban yawon tsoffin naira amma ya tsawaita wa’adin saboda matsin lamba daga ‘yan Najeriya.
Haka nan, kafin cikar wa’adin 10 ga watan Fabrairu, jihohin Kogi, Kaduna da Zamfara suka garzaya Kotun Koli, suka roƙi ta dakatar da CBN daga aiwatar da wa’adin.
Solacebase ta kawo maku rahoton yadda Kotun ta amince da buƙatar masu ƙara kana ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, 2023.
Tun bayan wannan hukuncin na Ƙotun koli, babban bankin ƙasa ya yi gum bai ce komai ba dangane da taƙamaiman lokacin haramta amfanin tsohon naira.
Sai dai wannan shiru na CBN ya jefa ‘yan Najeriya cikin ruɗani da waswasi kan matsayin tsohon takardun naira, wanda wasu suka fara daina karɓa amma a wasu wuraren ana karɓa.













































