Gwamnatin tarayya ta ayyana dakatarwar shekaru 3 ga masu satar jarrabawa

Tunji Alausa 750x430

Gwamnatin tarayya ta sanar da daukar tsauraran matakai na dakile matsalar satar jarrabawaR JAMB, inda ta yi gargadin cewa duk daliban da aka samu da laifin za su fuskanci hukuncin dakatar da su har na tsawon shekaru uku daga rubuta jarrabawar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da Sakandare JAMB, ta ce ministan ilimi Dakta Tunji Alausa, ya bayar da umarnin daukar matakin dakatar da makarantu ko kuma cibiyoyin rubuta jarrabawar JAMB ta na’ura kwamfuta da ke aikata laifuka.

A cewar mai bai wa hukumar JAMB shawara a fannin harkokin yada labarai Mista hukumar ta Fabian Benjamin, sabuwar manufar ta tanadi cewa za a soke irin wadannan cibiyoyi na musamman da ake kira da Miracle Centres na tsawon wasu shekaru, kamar yadda aka tsara.

Fabian Benjamin ya ce, sauran hukumomin shirya jarabawa da suka hada da WAEC, da NECO da kuma ta NABTEB za su sanya irin wannan takunkumi a lokaci rubuta nasu jarrabawar.

Baya ga takunkumin da hukumar JAMB ta fito da shi ta yi, sanya haramcin shekara uku daga shiga jarrabawar ga duk dalibin da aka samu da laifin magudi a rubuta jarabawar, inda kuma za a aiwatar da shi ta hanyar amfani da lambar shaidar dalibi ta shaidar dan kasa.

“Wannan umarni ya na cikin sashe na 16 (2) na dokar hana satar jarabawa,” in ji hukumar, inda ta bayar da misali da tanadin da ya bai wa kungiyoyin jarabawa damar yada sunayen wadanda suka aikata laifukan a tsakanin hukumomin jarrabawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here