Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa masu zuba jari na ƙasar Qatar cewa su kai masa rahoton duk wani jami’in Najeriya da ya nemi a ba shi cin hanci.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen taron kasuwanci da zuba jari tsakanin ‘ƴan kasuwar Najeriyar da masu zuba jarin na Qatar, da ke birnin Doha a ranar Lahadi.
Inda ya bayyana wa taron cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke neman kawo tsaiko ko kashe guiwar masu zuba jari a Najeriya.
Karin labari: Kamala Harris ta nemi a tsagaita wuta a Gaza
“Na zo nan ne domin na baku tabbacin cewa muna yin garambawul. Duk wata matsala da wasunku suka fuskanta a baya, ya riga ya wuce, ba za ku gamu da irinta ba a nan gaba,” in ji Tinubu.
Inda ya ƙara da cewa “Kada ku baiwa kowa a cikin mutane na cin hanci, idan kuma har sun nema ko sun karɓa a hannunku, ku kawo ƙararsu wurina. za ku samu ganina.”
Karin labari: Sudan ta buƙaci a mayar da ita AU kafin ta amince shiga tsakanin ƙungiyar
Tinubu ya kuma bayyana musu cewa kuɗadensu za su kasance cikin aminci, yana mai cewa gwamnatinsa ta ƙarfafa batun yaƙi da cin hanci da rashawa da yaƙi da rashin tsaro.
Ministan masana’antu da kasuwanci na Qatar, Sheikh Mohammed bin Hamad bin Qassim Al Abdullah Al Thani, ya bayyana cewa ƙasarsa na sa ran yin amfani da damar da Najeriyar ta bayar, inda Qatar ɗin za ta fi bai fifiko sun haɗa da zuba sabbin jari a shirye-shiryen da suka shafi rage iska mai gurɓata muhalli da ma’adanai da sinadaran da ake samu daga ɗanyen mai da kuma fannin masana’antu tare da kuma abubuwan ci.