Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, ta ce mutanen Gaza na cikin yunwa inda ta buƙaci Isra’ila ta ƙara yawan kayayyakin agajin da take bari a shiga da su zirin gaza.
Ta ce “dole a tsagaita wuta na aƙalla makonni shida” wanda a sa’ilin nan za’a iya fitar da duka ‘ƴan Isra’ilar da ake garkuwa da su.
Tun da farko, Isra’ila bata halarci taron tsagaita wutar da aka kira a Masar ba, tana mai cewa Hamas bata bayar da jerin sunayen waɗanda take garkuwa da su da har yanzu suke da rai ba.
Karin labari: Sudan ta buƙaci a mayar da ita AU kafin ta amince shiga tsakanin ƙungiyar
Hamas ta shaidawa BBC cewa ba ta samu damar yin hakan ba saboda ruwan bama-baman da Isra’ila.
“A zahiri da wuya mu gane waye ke da rai har yanzu,” a cewar Dakta Basem Naim, wani babban jami’in ƙungiyar.
Karin labari: Nikki Haley ta kayar da Trump a zaben fitar da gwani
Bayanai na nuna cewa tawagar Hamas da kuma masu shiga tsakani na Amurka da Qatar sun isa Alƙahira domin fara tattaunawa.
Ana ƙara matsin lamba don cimma tsagaita wuta, tun bayan al’amarin da ya auku a ranar Alhamis, inda aka kashe Falasɗinawa 112 a wajen birnin Gaza ta arewaci, bayan sunyi cuncurundo domin karɓar kayan agaji, inda sojin Isra’ila suka buɗe musu wuta.