
Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP ya fitar da jadawalin abubuwan da jam’iyyar zata yi gabannin zaɓen gwamna a jihar Ondo.
Hukumar zabe ta Najeriya ta sanya ranar 16 ga watan Nuwambar,2024, a matsayin ranar da za a yi zaɓen gwamna a jihar ta Ondo.
Jadawalin wanda ke ɗauke da sa hannun sakataren gudanarwar PDP na ƙasa Umar Bature, ya ce za’a yi zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar a ranar Alhamis 25 ga watan Afrilu, 2025.
Karin labari: Kashi 95 na masu akidar Boko Haram basa raye – Gwamnatin Borno
Haka kuma a ranar 9 ga watan Mayu ne kwamitin gunarwar jam’iyyar zai baiwa ɗan takarar mataimakin gwamnan takardar shaida.
Sannan ranar 20 ga watan na Mayu ce za ta kasance ranar ƙarshe na miƙa sunan wanda zai yiwa jam’iyyar takarar gwamna a jihar ga hukumar zaɓen ƙasar.
Jadawalin ya kuma ce ranar 10 ga watan Yuni za ta kasance ranar ƙarshe ta musanya sunan ɗan takara.












































