Gwamnatin tarayya- Za mu bunƙasa wasannin masu buƙata ta Musamman

images
images

Ministan matasa da wasanni na Najeriya Sunday Dare, ya ce,  gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa harkokin wasannin masu buƙata ta musamman.

Ministan, ya bayyana hakan ne a daren jiya Asabar yayin zantawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan ya ƙaddamar da gasar wasannin masu buƙata ta musamman karo na farko, watau First maiden National Para Games wadda aka ƙaddamar a filin wasa na Moshood Abiola, da ke birnin tarayya Abuja.

Dare, ya ƙara da cewa duk da matsalolin rashin kuɗaɗen gudanar da gasar, amma hakan bai sanya sun yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙaddamarwar la’akari da yadda aka ƙirƙiri sabon sashen wasannin masu buƙata ta musamman a watan Disamba bara.

Haka zalika ya ce, “Ya zama wajibi mu yi duk mai yiwuwa wajen bunƙasa wannan wasanni na masu buƙata ta musamman.

Ministan ya kuma ce, “A baya-bayan nan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya kafa sabuwar ma’aikata ta masu buƙata ta musamman, don haka lokaci ya yi da kamfanoni zasu shigo a haɗa hannu da gwamnati don ci gaba da bunƙasa wasannin a gaba, kuma tilas mu godewa Alhaji Aliko Dangote saboda gudunmowar da yake bawa wasanni” inji Sunday Dare.

Rahotonni sun bayyana cewa jihohi 21 ne suka shiga gasar wadda za a fara gudanar da ita yau Lahadi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here