Gidan rediyon Fresh FM mai zaman kansu da ke garin Ibadan da ke jihar Oyo, ya fuskanci hari daga wasu ƴan fashi da makami da sanyin safiyar Lahadi.
Rahotonni sun bayyana cewa, gidan rediyon na tsaka da yaɗa shirye-shiryen kai tsaye lokacin da ƴan bindigar suka kai masa farmakin.
Wani ma’aikacin gidan rediyon ya shaida wa jaridar Punch cewa ƴan fashin sun kai farmaki gidan rediyon wanda ya ke a unguwar Challenge da misalin ƙarfe 6:30 na safe.
“Babu mutuwa, Babu wanda ya samu rauni, kawai sun tafi da kayayyaki masu daraja,” inji shi.
Sai dai majiyarmu ba ta samu jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Adewale Osifeso, game da faruwar lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoton.












































