Majalisar Wakilai ta magantu tsakanin Hukumar PSC da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda kan daukar aiki a rundunar.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisar wakilai Mitema Obordor na jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa ya gabatar a zaman majalisar a Abuja.
Taken kudirin mai suna: “Gabatar da Matsala: Bukatar Gaggawa don Bincike da sasanta Rikicin daukar ‘Yan Sanda Dake Dakatar Da daukar aikin ‘yan sanda na 2023/2024.
Obordor ya gabatar da bukatar cewa ‘yan sandan Najeriya na karkashin kulawar PSC wadda ke da ikon nadawa, karin girma da korar duk jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) in ban da IGP.
Karin labari: Wata motar man fetur ta kama da wuta a gidan man Mainland a Abuja
Wannan, in ji shi, yana da manufar kulla alakar amana da amincewa tsakanin jama’a da ‘yan sanda.
Ya ce idan aka yi la’akari da yawan al’ummar Najeriya da kuma yanayin tsaro a kasar, ya kamata a ce ma’aunin ‘yan sanda da ‘yan kasa a Najeriya ya kamata ya zama dan sanda daya zuwa 200.
Sai dai ya ce kasar a halin yanzu tana da rabon dan sanda daya da ‘yan kasar 650, wanda hakan ke nuna gazawa sosai a bangaren ‘yan sandan Najeriya.
Wannan, in ji shi, ya yi ƙasa da shawarar Majalisar Dinkin Duniya na ɗan sanda ɗaya ga ‘yan ƙasa 450.
Karin labari: Doguwa ya fice daga APC
Ya ce takaddamar da ta kunno kai tsakanin hukumar ta PSC da I-GP, ta haifar da cikas, kuma an dakatar da aikin daukar ma’aikata da ake yi na kusan watanni 10;
Ya ce akwai matukar bukatar karfafa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta hanyar sanya rabon dan sanda daya ga ‘yan kasa 200.
Ya ce ya zama wajibi a yi amfani da shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar na rabon dan sanda daya ga ‘yan kasar 450 domin tunkarar kalubalen tsaro da ke addabar kasarmu.
Ya kara da cewa karancin jami’an ‘yan sanda ya rage yawan ‘yan sanda a cikin al’ummomi, wanda hakan ya haifar da karuwar laifuka yayin da masu aikata laifuka ke cin gajiyar lamarin.
Karin labari: Dangote yayi alkawarin bunkasa cibiyoyin harkokin ilimi guda 10
Da take amincewa da kudirin, majalisar ta bukaci kwamitocinta na ‘yan sanda da su binciki musabbabin takaddamar da ta kunno kai tsakanin PSC da I-GP.
Wannan, in ji shi, da nufin warware takaddamar, kuma an ci gaba da aikin daukar ma’aikata ba tare da bata lokaci ba, da kuma gabatar masa da shawarwari cikin makonni hudu.
Majalisar ta kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da isassun kudade da kayayyakin da ake bukata don tallafawa daukar aiki da horar da ‘yan sanda.
Haka kuma ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara yawan ‘yan sandan da za a dauka aiki tare da yin hakan ta tabbatar da tanade-tanaden da’a na tarayya kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada sosai a ruwayar NAN.