Wata motar man fetur ta kama da wuta a gidan man Mainland a Abuja

Gobara, motar, man, fetur, tashi, gidan, Mainland, Abuja, wuta, kama
Gobara ta kone wata tankar mai a tashar Mainland Oil da Gas da ke mahadar Dutse daura da babbar titin Kubwa a Abuja. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN...

Gobara ta kone wata tankar mai a tashar Mainland Oil da Gas da ke mahadar Dutse daura da babbar titin Kubwa a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yamma a ranar Alhamis.

Karin labari: Doguwa ya fice daga APC

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yana shirin yin layi na neman mai a gidan man sai wani ya yi kururuwar cewa wata motar dakon mai da har yanzu bai sauke mai ba ta kama da wuta.

NAN ta rawaito cewa an aike da jami’an tsaro da na kashe gobara don kashe gobarar da ta afku a yankin, da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, kamar yadda har bayan kashe gobarar ba a samu rahoton asarar rayuka ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here