Ganduje ya taya Injiniya Ramat murnar samun lambar yabo daga Kasar Dubai

IMG 20220724 WA0247 750x430 1
IMG 20220724 WA0247 750x430 1

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya shugaban karamar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat, bisa kasancewarsa daga cikin shugabanni matasa 50 masu fada a ji a Afirka, wanda kuma ya samu lambar yabo ta Nasara, daga mai martaba Sarkin Dubai Sheikh Rashid Bin Majid Al-Mu’alla.

“Mun fahimci cewa a taron gidauniyar Pan African Youth Leadership Foundation wanda ya gudana a Dubai baya-bayan nan, namu kuma shugaban karamar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat, mai himma ne, ya zama abin koyi ga matasa a nahiyar Afirka,” in ji Ganduje.

Sanarwar da babban sakataren yada labaran sa, Abba Anwar, ya fitar a Kano, ranar Alhamis, ta ce duka zabin da kuma lambar yabo, a cewar gwamnan “…ba kawai abin farin ciki ba ne, shaida ce ta duniya da kuma shaida cewa Injiniya Ramat ya yi fice wajen gudanar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummarsa.”

“Gwamna Ganduje ya kara da cewa, kasancewarsa kwararre a fagen gudanar da ayyuka, Ramat zai bar tarihi mai kyau don wasu su bi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here