NiMet ta yi gargadin fuskantar tsananin zafi a jihohin Gombe, Kano, da sauran su

NiMet 750x430

Hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMet) ta yi gargadi kan tsananin zafi a jihar Gombe da wasu jihohin Arewa 17.

Sauran jihohin sun hada da Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Bauchi, Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Niger, Kogi, Nasarawa, Benue, da kuma babban birnin tarayya.

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton yanayin da aka fitar a ranar Juma’a kuma Manajan hasashen yanayi na jihar Gombe, Gayus Musa ya mika wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Gombe ranar Asabar.

Karin karatu: Dalilin da ya sa muka ziyarci Buhari a Kaduna – Atiku

Hukumar ta ce ana sa ran zafin zai tashi zuwa ma’aunin celcius 40 daga ranar Asabar, lamarin da zai haifar da rashin jin dadi a jihohin da abin ya shafa.

Musa ya bukaci mazauna Gombe da su dauki matakan da suka dace domin tsananin zafi yana da illa ga lafiya.

Ya shawarci mazauna yankin da su guji yawan shiga rana tare da neman wurare masu sanyi tare da ba da shawarar shan ruwa mai yawa da kuma guje wa ayyuka masu tsanani a lokacin mafi zafi na yini.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su kara wayar da kan jama’a game da hadarin zafi da kuma matakan kariya masu mahimmanci ga rayuwa.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here