Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, ya bukaci shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ya janye kansa daga binciken da ake yi masa, yana bayyana binciken a matsayin wanda aka yi da son rai na siyasa.
Wannan bukata na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin Malami kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa matakin binciken da tsare shi ya samo asali ne daga sabani na kashin kai bayan Malami ya sauya sheƙa zuwa ADC.
Malami ya bayyana cewa shugaban EFCC na da tsohuwar gaba da shi tun daga lokacin da kwamitin binciken shari’a na Ayo Salami ya binciki zarge-zargen cin hanci a cikin EFCC a lokacin da yake rike da mukamin babban lauyan ƙasa.
Ya nuna cewa yadda ake tafiyar da binciken, ciki har da tsare-tsare ba bisa ka’ida ba, matsin lamba ta kafafen yaɗa labarai da karya dokokin aiki, duk sun nuna alamun ramuwar gayya ta kashin kai, yana mai cewa EFCC a ƙarƙashin shugabancinta na yanzu ba za ta iya gudanar da bincike cikin adalci da tsaka-tsaki ba.
Karin labari: Har yanzu Malami bai cika sharuɗɗan beli ba – EFCC
Malami ya bukaci a sauke shugaban EFCC daga kula da lamarin tare da mika shi zuwa wata hukuma ta gwamnati domin tabbatar da adalci, sahihanci da amincewar jama’a ga tsarin shari’a.
Ya kuma bukaci babban lauyan gwamnatin tarayya na yanzu ya shiga tsakani, yana gargaɗin cewa ci gaba da sa hannun shugaban EFCC zai iya janyo illa ga hukumomi da kuma cin zarafin ikon gurfanarwa.
Haka kuma Malami ya nemi a gurfanar da shi gaban kotu cikin gaggawa kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada, yana jaddada cewa kotu ce kawai ke da ikon halaccin yanke hukunci, ba wata hukuma da ake zargin tana karkata ta siyasa ba.
Ya kuma zargi EFCC da shirin amfani da shaidu masu sarkakiya domin gina shari’a a kansa, yana mai cewa manufarsa ita ce wanke sunansa ta hanyar doka da adalci ba tare da siyasantar da yaki da cin hanci ba.












































