Yanzu-yanzu: Ana Zargin ‘Yan sanda sun kama shugaban kungiyar Kwadago, Joe Ajaero

Joe Ajaero (1)
Joe Ajaero (1)

Ana kyautata zaton ‘Yan sanda sun kama shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero.

Rahotanni na nuni da cewa ‘Yan sandan sun kama shi ne a Owerri, babban birnin jihar Imo a dai-dai lokacin da yake tsaka da shirya wata zanga-zangar nuna adawa ga kin biyan albashin ma’aikata a jihar.

An kama Ajaero ne da misalin karfe 8 na safiyar Laraba 1 ga watan Nuwambar 2023, yayin da ma’aikata suka fara taruwa a sakatariyar kungiyar ta NLC dake jihar domin gudanar da zanga-zangar, kwatsam wasu mutane dauke da muggan makamai suka afkawa Sakatariyar, suka kuma far wa ma’aikatan tare da fatattakar su.

Sai dai daga bisani ma’aikatan sun sake haduwa a Sakatariyar karkashin jagorancin Shugaban kungiyar kwadagon da kuma sakatare janar na kuingiya Emma Ugboaja tare kuma da fara zanga-zangar.

A daidai lokacin da Ajaero ke shirin yin jawabi, sai ga jami’an ‘yan sanda dauke da makamai suka kama shi suka tafi da shi tare da wasu shugabannin kungiyar ta NLC.

Tuni dai Daraktan yada labarai na kungiyar ta NLC, Benson Upah ya tabbatar da faruwar lamarin.

Shima da yake bayyana yadda lamarin ya faru, mataimakin sakataren kungiyar, Chris Onyeka ya bayyana cewa yana tare da Ajaero lokacin da ‘Yan sanda suka kama shi, tare da tafiya da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here