Tsohon Minista, Nwabueze ya rasu yana da shekaru 94

Prof. Ben Nwabueze
Prof. Ben Nwabueze

Tsohon Ministan Ilimi kuma lauya, Farfesa Ben Nwabueze ya rasu.

Ya rasu ne a ranar Lahadi yana da shekaru 94, kamar yadda dansa, Eni Nwabueze, MD, ya bayyana a wata sanarwa.

Nwabueze ya fito ne daga Atani a karamar hukumar Ogbaru a jihar Anambra.

Nwabueze ya kasance Sakatare Janar na Ohanaeze Ndigbo a duk duniya kuma Babban Lauyan Najeriya (SAN).

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Cikin bakin ciki, muna sanar da rasuwar ubangidanmu, Farfesa B. O. Nwabueze SAN, NNOM, CON, babban sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo da Oduah Afo-na-isagba na Atani, jihar Anambra. , ranar Lahadi, Oktoba 29, 2023, yana da shekara 94.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here