Mambobin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya reshen jihar Sokoto (PASAN) a ranar Litinin sun bi sahun takwarorinsu na kasa baki daya a yayin da suka shiga yajin aiki na sai baba ya gani, tare da rufe harabar majalisar dokokin jihar.
Shugaban kungiyar, Abubakar Yusuf, yayin da yake zantawa da manema labarai a Sokoto ya bayyana cewa yajin aikin wani tsawaita fafutuka ne da suka fara a shekarar 2020.
Ya ce, “Kamar yadda za ku iya tunawa, mun dauki irin wannan matakin ne a shekarar 2020. Bayan shiga tsakani daga bangarori daban-daban, mun cimma yarjejeniya da ta yi alkawarin ba da cikakken ‘yancin cin gashin kai ga bangaren majalisar dokoki.