Da Dumi-dumi: Kotun Koli ta sake tabbatar da Laila Buhari a matsayin ‘yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar PDP

LailaBuhari 635x430 1
LailaBuhari 635x430 1

Kotun koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin ‘yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar PDP.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a baya ma kotun daukaka kara ta tabbatar da Laila Buhari a matsayin Yar takarar inda ta soke zaben Danburan Nuhu.

A hukuncin da kotun kolin ta yanke wanda mai shari’a Muhammad Lawal Garba ya karanta, ta yi watsi da dukkan dalilan daukaka karar, da Danburam Nuhu, ya yi.

A yayin yanke hukuncin Mai shari’a Garba yana tare da Justice Kudirat Kekere Ekun da Justice Saulawa sai Justice Ibrahim Jauro, da kuma Justice Emmanuel Agim.

Muna tafe da garin bayanai nan gaba…..

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here