Yanzu-Yanzu: CBN Ya Umarci Bankunan kasuwanci da su rinka biyan sabbin kuɗi da akan Kanta

New Naira notes sabo 750x430 1
New Naira notes sabo 750x430 1

Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan kasuwanci da su fara biyan kudaden da aka sauyawa fasali a kan Kanta, idan har bai haura Naira 20,000 a kowace rana ba.

Daraktan Sadarwa da watsa labarai na babban bankin, Osita Nwanisobi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa babban bankin zai hada gwiwa da hukumar ‘yan sandan Najeriya da hukumar tara haraji ta tarayya FIRS sai hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da kuma sashin kula da harkokin kudi na Najeriya NFIU, don hukunta masu masu sayar da sabbin kuɗi a bankuna.

Ya ce: “Babban Bankin Najeriya CBN ya lura, tare da nuna matukar damuwa, ganin yadda mutane ke sayar da sabbin takardun kudi da aka yi wa gyaran fuska lamarin da ya jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here