Zamfara: Gwamna Lawal ya ba da umarnin rufe kasuwa nan take bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a fadar sarki

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

Wasu ‘yan bindiga da dama sun kai hari fadar Sarkin Maru Abubakar Gado Maigari inda suka kashe wani mai gadin fadar a daren Laraba.

‘Yan bindigan sun sake komawa fadar a daren Alhamis da nufin kashe ko kuma sace sarkin amma suka kai farmaki kan jama’a ba su ji ba ba su gani ba lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu.

Sarkin a cewar majiyar mu da kyar ya tsallake rijiya da baya a harin da ‘yan bindigan suka kai a ranar Laraba da Alhamis da daddare

An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun yi yunkurin yin garkuwa da Sarkin bai yi nasara ba, inda suka rika kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a lokacin da suka je gida gida suna neman mazauna garin da nufin yin garkuwa da su.

Harsashin bindiga da dama ya janyo hasarar ababen hawa da wasu kayayyaki masu daraja, sannan kuma an jikkata wasu mutanen yankin da ba a san adadinsu ba a yayin aikin.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Munnir Hidara ya sanyawa hannu ya yi Allah wadai da harin tare da bayyana shi a matsayin dabbanci da rashin mutuntaka.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin rufe kasuwar Maru Weekly ba tare da bata lokaci ba, har sai an daidaita matsalar tsaro a karamar hukumar.

Manufar ita ce a wargaza duk wani shiri na ta’addanci na kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba gani ba a kasuwa hari, tare da samar da karin na’urori da za su taimaka wa gwamnati da hukumomin tsaro wajen yakar masu aikata laifuka.

A farkon shekarar nan ne aka kai hari a hedikwatar ‘yan sanda da ke karamar hukumar Maru, kuma an kashe wani DPO da wasu jami’ai a wani shingen bincike na ‘yan sanda.

Maru na daya daga cikin manyan kananan

An yi jana’izar wadanda ‘yan bindiga suka kashe a ranar Juma’a da rana a karamar hukumar Maru

Har yanzu dai hukumomin ‘yan sanda a Zamfara ba su ce uffan ba kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here