A ranar Juma’a ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2024 na Naira biliyan 350 ga majalisar dokokin jihar, tare da yin alkawarin bin hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da tsantseni, da rikon amana, da kuma gaskiya.
Yusuf ce adadin kudaden da zaa kashe ya kai Naira biliyan 357.9, yayin da ake sa ran samun kudaden shiga a cikin gida ya kai Naira biliyan 100.7, inda ya kara da cewa babban jarin da ake sa ran zai samu ya kai Naira biliyan 39.265, wanda ya haura Naira biliyan 4.9 a shekarar 2023 wanda ke nuna raguwar kashi 12.53 cikin dari.