Mutane 20 ne suka jikkata yayin da tankar mai ta fashe a Kaduna

Fire outbreak.jpeg
Fire outbreak.jpeg

Akalla mutane 20 ne suka samu raunuka daban-daban biyo bayan fashewar wata tankar mai a gidan mai da ke unguwar Rigasa a Kaduna.

Mista Paul Aboi, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kaduna ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a Kaduna.

Aboi ya ce daga cikin wadanda suka jikkata akwai jami’an kashe gobara na tarayya biyar, da wasu ma’aikatan hukumar ‘yan banga ta Kaduna, da kuma masu wucewa.

Daraktan ya ce jami’an kashe gobarar da suka jikkata a halin yanzu suna karbar kulawa a asibitin kwararru na Barau Dikko da ke Kaduna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here