Yawan wutar lantarkin da Najeriya ke samarwa ya faɗo daga megawatts 2,917.83 zuwa megawats 1.5 a tsakanin ƙarfe 11 da 12 na safiyar ranar Larabar nan.
Jim kaɗan bayan lalacewar, shafin na babban layin wutar Najeriya na X ya bayar da muhimman bayanai dangane da al’amarin inda ya ce aikin ƙoƙarin shawo kan matsalar na ci gaba.
Rahoton ya nuna cewa dukkan kamfanonin rarraba wuta (DisCos) a faɗin ƙasar sun daina karɓar wuta gaba ɗaya, banda Ibadan DisCo da ke karɓar 20MW kacal. Misali, Abuja, Kano, Kaduna, Jos, Enugu, da sauran DisCos sun dawo da 0MW.
Wannan matsalar ta sake janyo cikas ga harkokin yau da kullum, inda masu sana’o’in nama, kifi, kaji da sauran kayayyaki masu buƙatar firji suka yi asara mai yawa, musamman a biranen Arewa.
A wani jawabi da ta fitar, Abuja DisCo ta shaida wa kwastomominta cewa matsalar daukewar wutar ta samo asali ne daga rasa wutar da ake samu daga gidan wuta na ƙasa da ƙarfe 11:23 na safe.
Kamfanin ya kuma tabbatar da cewa yana aiki tare da sauran hukumomi domin dawo da tsarin wuta cikin gaggawa, tare da neman haƙuri da juriya daga jama’a har zuwa lokacin da za a daidaita wutar.













































