Hajjin bana: Mahajjaciya ƴar jihar Kano ta rasu a Makkah

1688572443805
1688572443805

Hukumar Jin dadin alhazai ta jihar kano ta tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya mai suna Hadiza Isma’il, yar asalin karamar hukumar Madobi a kasar Saudiyya.

Hadiza Isma’il, daga karamar hukumar Madobi ta rasu a ranar Litinin da misalin karfe 3:15 na rana agogon Saudiyya bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya, in ji sanarwar da ga Sanusi Bature Dawakin-Tofa, shugaban tawogar manema labarai na Hajjin bana.

Sanarwar ta ce an kai matar, mai shekaru 58 a asibitin NAHCON domin jinyar zazzabi kafin a kai ta asibitin Sarki Abdulaziz dake Makka inda aka tabbatar da rasuwarta.

Tuni dai aka binne ta a garin Makka bayan sallar jana’iza a masallacin Harami na Makkah.

Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ya mika ta’aziyyar hukumar ga iyalan mamaciyar a madadin gwamnan jihar Kano, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama ya kuma baiwa iyalai hakurin jure rashin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here