Babban sakataren OPEC Sanusi Barkindo ya rasu yana dan shekara 60

OPEC Secretary General Barkindo 587x430 1
OPEC Secretary General Barkindo 587x430 1

Allah Ya yi wa Babban Sakataren Kungiyar kasashen da ke arzikin man fetur, OPEC, Dr Muhammad Sanusi Barkindo rasuwa a ranar Talata da daddare.

Rasuwarsa ta zo farat ɗaya, inda ko a ranar Talatar da rana ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja, tare da tawagar shugabannin Kungiyar OPEC.

Margayi Sanusi Barkindo na shirin sauka saga mukaminsa na sakataren OPEC bayan shafe shekaru shida a kan kujerar.

Shugaban Kamfanin mai na Najeriya, NNPC, Malam Mele Kyari ne ya sanar da rasuwar marigayi Barkindo a wani sakon da ya wallafa ranar Laraba da asuba a shafinsa na Twitter.

Ana sa ran yin za a fitar da bayanai game da shirin jana’izar margayin a ranar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here