Obasanjo ya bayyana yadda marigayiyar matarsa ta sa a sake shi daga kurkuku

Olusegun, Obasanjo, Batun, sakin, Nnamdi Kanu, gwamnonin, Kudu maso Gabas
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa batun sakin Nnamdi Kanu baya cikin tattaunawarsa da gwamnonin Kudu maso Gabas a jihar Enugu ranar...

 

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda marigayiyar matarsa, Stella Obasanjo, ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an sake shi daga kurkuku.

Ya yi wannan bayani ne yayin ƙaddamar da asibitin Stella Obasanjo mai gadaje 250 a Benin, babban birnin Jihar Edo.

Obasanjo ya kasance a kurkuku a lokacin mulkin Janar Sani Abacha, bisa zargin yunkurin juyin mulki.

Amma bayan rasuwar Abacha, gwamnatin Janar Abdulsalami Abubakar ta sake shi, wanda daga baya ya zama shugaban ƙasa.

Stella Obasanjo, wadda ‘yar asalin Jihar Edo ce, ta yi ƙoƙari sosai don ganin an sake shi.

Daga bisani ta zama uwargidan shugaban ƙasa, amma ta rasu a lokacin wa’adin mulkinsa na biyu.

Yayin tuna sadaukarwarta, Obasanjo mai shekara 87, ya bayyana godiyarsa, inda ya ce, “Marigayiyar matata ta tafi ko’ina don ganin na fito daga kurkuku da rai. Ta tafi Vatican City, Faransa da wasu ƙasashe. Ba a iya ba ta kowane irin yabo daidai da rawar da ta taka.”

Ya nuna godiyarsa ga sabon asibitin da aka keɓe da sunanta, tare da yaba wa Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, bisa ƙoƙarin da ya yi na kammala aikin.

Ya kuma tuna alaƙarsa da tsohon gwamnan Edo, John Odigie Oyegun, wanda ya yabawa matsayin kwararren jami’in gwamnati.

“Tare da wannan asibiti, za ku samu magani mai inganci a kan kowace irin cuta,” in ji Obasanjo.

“Ina fatan Allah ya ƙara wa gwamnan albarka da ƙarfafa masa guiwa bisa kammala wannan gagarumin aiki.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here