Rundunar ‘yan sada sun tabbatar da mutuwar wani dan shekara 39, wanda ya kashe kansa, yayin da hukumar yaki da safarar dan’adam NAPTI ta garkameshi.
Wanda ake zargin ankamashine a karamar hukumar Ikeja da ke jihar Lagos, bisa zargin sa da safarar dan Adam.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Lagos, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar al-amarin ranar Litinin, inda yace an garzaya da gawar asibiti.
Ya kuma tabbatar da cewa rudunar ‘yan sandan zata cigaba da bincike akan faruwar lamarin.













































