Kwamitin raba asusun tarayya (FAAC), ya raba Naira tiriliyan 1.678 a tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi na watan Fabrairu.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da FAAC ta fitar kuma Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ofishin Akanta-Janar na kasa (OAGF) Bawa Mokwa ya sanyawa hannu.
A cewar sanarwar, jimillar kudaden shiga na Naira Tiriliyan 1.678 ya kunshi kudaden shiga na doka na Naira 827.633 da kuma kudaden harajin kayayyaki (VAT) na Naira 609.430.
Har ila yau, ta ƙunshi kudaden shiga na hada haɗar kiran waya na Naira biliyan 35.171, kudaden shiga na ma’adanai na Naira biliyan 28.218 da kuma ƙara Naira biliyan 178.
Karanta: Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta bayyana matsayarsu kan dokar ta-baci a Rivers
Ya ce an samu jimillar kudaden shiga na Naira tiriliyan 2.344 a cikin watan Fabrairu.
Sanarwar ta ce, an samu jimillar kudaden shiga na Naira Tiriliyan 1.653 na watan Fabrairu, wanda ya yi kasa da Naira Tiriliyan 1.848 da aka samu a watan Janairu da Naira Biliyan 194.664.
Ya ce an samu babban kudaden shiga na Naira biliyan 654.456 daga VAT a watan Fabrairu, kasa da Naira biliyan 771.886 da aka samu a watan Janairu da Naira biliyan 117.430.
Sanarwar ta ce daga cikin kudaden shigar da ake rabawa na Naira Tiriliyan 1.678, Gwamnatin Tarayya ta samu jimillar Naira Biliyan 569.656, sannan gwamnatocin Jihohin kasar nan sun samu jimillar Naira Biliyan 562.195.
Ya ce kananan hukumomi sun samu jimillar Naira biliyan 410.559, kuma an raba jimillar Naira biliyan 136.042 (kashi 13 na kudaden shiga na ma’adinai) ga jihohin da suka amfana a matsayin kudaden shiga.
A cewar sanarwar daga kudaden harajin VAT na Naira biliyan 609.430, gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 91.415, gwamnatocin jihohi kuma sun karbi Naira biliyan 304.715, sai kuma kananan hukumomin da suka samu Naira biliyan 213.301. (NAN)