Kotu ta ci tarar Naira Miliyan 1 a kan gwamnatin Kano a shari’ar motocin tsoffin kwamishinoni

Kano seized official vehicles

Babbar kotun masana’antu ta Najeriya, reshen shari’a na Kano, a ranar Talata ta dage sauraron karar da wasu tsoffin kwamishinonin Jihar Kano suka shigar domin hana gwamnatin jihar kwato motocin gwamnati da aka ba su yayin da suke kan mukami.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kotun, karkashin jagorancin Mai shari’a Mahmood Abba Namtari, ta kuma yanke hukuncin biyan kudin tara Naira dubu 200 kan wadanda ake kara a kowace daga cikin shari’o’i biyar bayan lauyansu ya nemi a dage zaman domin su samu damar gabatar da takardun da ake bukata.

A zaman kotun da aka sake gudanarwa, lauyan gwamnatin Jihar Kano, Barista S. U. Jibril, ya sanar da kotun cewa wadanda ake kara ba su shirya ci gaba da sauraron karar ba.

Ya bayyana wa kotun cewa ofishin wanda ake kara na farko ne kawai ya tuntube shi da yammacin ranar Litinin, don haka bai samu isasshen lokaci da zai shirya takardun da ake bukata ba.

Sai dai lauyan tsoffin kwamishinonin, Suraj Sa’ed, SAN, ya bayyana cewa ba su da wata matsala kan bukatar dage zaman, amma ya roki kotun ta sanya kudin tara domin diyya ga masu karar.

Sa’ed ya bukaci kotun ta sanya tarar Naira miliyan 1 a kowace daga cikin shari’o’in, yana mai cewa an riga an mika wa wadanda ake kara takardun kotu don haka ya kamata su shirya amsarsu.

A nasa bangaren, lauyan gwamnati ya kalubalanci bukatar sanya kudin tara, yana mai cewa har yanzu wadanda ake kara suna cikin lokacin da doka ta tanada domin gabatar da takardunsu.

Sai dai Mai shari’a Namtari ya bayyana cewa bayanan kotu sun nuna cewa an riga an mika wa wadanda ake kara takardun tun a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Duk da adawar da aka yi kan bukatar kudin tara, kotun ta yanke hukuncin biyan Naira dubu 200 kan wadanda ake kara a kowace daga cikin shari’o’i biyar tare da dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Afrilu 2026 domin ci gaba da sauraro.

Tsoffin kwamishinonin da suka shigar da karar sun hada da Dr Yusuf Ibrahim K/Mata, tsohon kwamishinan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire; AVM Ibrahim Umar mai ritaya, tsohon kwamishinan tsaron cikin gida; Nasir Sule Garo, tsohon kwamishinan ayyuka na musamman; Adamu Aliyu Kibiya, tsohon kwamishinan harkokin jin kai da rage talauci; da Mustapha Rabi’u, tsohon kwamishinan matasa.

Tsoffin kwamishinonin sun garzaya kotu suna neman a hana gwamnatin Jihar Kano kwato motocin gwamnati da aka ba su yayin da suke kan mukamansu.

Sun kuma lissafa babban lauyan Jihar Kano, gwamnan Jihar Kano da kuma hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano a matsayin wadanda ake kara.

A zaman kotun da ya gabata, kotun ta yi watsi da bukatun gaggawa daban-daban da masu karar suka gabatar domin a dakatar da gwamnati daga daukar matakin kwato motocin.

Mai shari’a Namtari ya ki amincewa da bukatun, inda ya umurci a saurari karar tare da sanar da wadanda ake kara domin su gabatar da hujjojinsu kafin a yanke wani hukunci na wucin gadi.

Takaddamar na daga cikin shari’o’in da ke gudana tsakanin gwamnatin Jihar Kano da wasu tsoffin kwamishinoni kan ko suna da hakkin ci gaba da rike motocin gwamnati da aka ba su yayin da suke kan mukami.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here