Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana rikicin cikin gida da kuma takaddamar shari’a da ke gudana a jam’iyyar PDP a matsayin babban dalilin da ya sa ya sauya sheka daga jam’iyyar.
Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Mallam Mani Mummuni, ne ya sanar da sauya shekar a hukumance ranar Litinin bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Gusau.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana sauya shekar daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC a matsayin mataki da ya zama dole domin amfanin al’ummar Jihar Zamfara gaba daya.
Sanarwar ta bayyana cewa shiga APC wata shawara ce da masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara suka yanke sakamakon kalubalen shari’a da jam’iyyar PDP ke fuskanta.
Karanta: Yanzu-yanzu: Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya fice daga PDP zuwa APC
A cewar sanarwar, gwamna Dauda Lawal ya sauya sheka daga PDP zuwa APC bayan shawarar da dukkan masu ruwa da tsaki suka amince da ita a Jihar Zamfara.
Sanarwar ta kara da cewa gwamna Dauda Lawal ya nuna cikakken jajircewa ga jam’iyyar PDP, inda ya yi kokari wajen sulhunta bangarorin jam’iyyar domin tabbatar da hadin kai da kuma damar tsayar da ‘yan takara a zabuka masu zuwa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa kokarin samar da zaman lafiya da sulhu da kuma warware matsalolin ba tare da zuwa kotu ba ya gamu da kalubale, lamarin da ya haifar da jerin shari’o’i da ka iya yin tasiri a nan gaba, musamman ga shugabannin da za su tsaya takara a zaben shekarar 2027.
Ta kara da cewa gwamna Lawal shi ne mutum na karshe da ya ci gaba da tsayawa a jam’iyyar PDP har zuwa lokacin da hukuncin kotun daukaka kara ya fito.
Haka kuma shi ne kadai gwamnan da ke neman wa’adi na biyu da ya zabi ci gaba da kasancewa a jam’iyyar, yana fatan shugabannin jam’iyyar za su dauki matakin da ya dace.
Sanarwar ta ce a wasu jerin tarurruka da suka dauki makonni ana yi, gwamna Lawal ya sanar da masu ruwa da tsaki cewa ya fahimci bukatarsu ta komawa APC, amma zai yanke hukunci ne bayan hukuncin kotun daukaka kara.
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta daukaka kan hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Mai shari’a James Omotosho, ya yanke a ranar 31 ga watan Oktoba, wanda ya hana hukumar INEC amincewa da sakamakon babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba.
Hukuncin kotun daukaka kara ya kawo karshen zaman gwamna Dauda Lawal a jam’iyyar PDP, inda ya zabi shiga jam’iyyar APC domin ci gaba da aiwatar da shirin ceto da sake gina Jihar Zamfara.













































