Hukumar kashe gobara ta tarayya ta shawo kan wata gobara da ta tashi da tsakar dare a otel din De Bently da ke Utako a Abuja, inda ta hana wutar yaduwa zuwa wasu gine-ginen da ke makwabtaka da wurin.
Lamarin ya faru ne da daren ranar Litinin a wani ginin kasuwanci mai hawa hudu wanda ke da fadin kusan murabba’in mita 500.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na kasa kuma shugaban sashen ayyukan kamfani na hukumar kashe gobara ta tarayya, Paul Abraham, ya bayyana cewa an samu rahoton tashin gobarar da karfe 20:28 na dare.
Sanarwar ta ce jami’an kashe gobara daga tashar Wuse sun garzaya wurin cikin gaggawa kuma sun isa wurin da karfe 20:38 domin fara aikin kashe gobarar karkashin jagorancin babban kwamandan hukumar.
Babban kwamandan hukumar kashe gobara ta tarayya, Olumode Adeyemi, ne da kansa ya jagoranci aikin daukar matakin gaggawa.
Rahotanni sun nuna cewa an shawo kan gobarar ta hanyar hadin gwiwar jami’ai da suka yi amfani da bututun ruwa da dama da kuma motocin kashe gobara.
Rahoton farko ya nuna cewa wata kila fashewar iskar gas ce ta haddasa gobarar, amma har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin lamarin ba.
Sanarwar ta ce kimanin darajar kadarorin da ke cikin wurin ta kai kusan Naira Biliyan 1, inda aka samu nasarar ceton kadarori na kusan Naira Miliyan 650, yayin da gobarar ta lalata kadarori da darajarsu ta kai kusan Naira Miliyan 350.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba a samu asarar rayuka ko raunuka ba a lokacin faruwar lamarin.
A cewar sanarwar, jami’an ‘yan sanda da wasu sassan jami’an kashe gobara sun halarci wurin domin samar da tsaro da kuma tallafawa aikin kashe gobarar.
Babban kwamandan hukumar ya yabawa jami’an nasa bisa saurin daukar mataki da kuma kwarewar da suka nuna, yana mai cewa matakin da suka dauka ya taimaka wajen hana gobarar zama babbar masifa.
Tuni an kuma tura tawagar masu binciken gobara domin gano musabbabin tashin gobarar kai tsaye da kuma dalilan da suka haifar da ita.
Hukumar kashe gobara ta tarayya ta kuma bukaci masu otel, ‘yan kasuwa da sauran jama’a da su rika bin dokokin tsaron gobara musamman wajen kula da silindar gas da sauran abubuwan da ke iya kama da wuta, tare da jaddada muhimmancin sanar da hukumomi cikin gaggawa domin rage barnar da ka iya faruwa.













































