Ni na kara wa kaina maki a jarrabawar JAMB – Mmesoma

Anambra panel reveals how Mmesoma forged result.jpeg
Anambra panel reveals how Mmesoma forged result.jpeg

Ejikeme Mmesoma mai shekarar 19, wadda tsohuwar ɗaliba ce a makarantar ‘Anglican Girls’ Secondary School’ a jihar Anambra, ta bayyana yadda ta kara wa kanta maki a takardar sakamakon jarrabawar.

A ‘yan kwanakin nan, batun ya janyo ce-ce-ku-ce, tun bayan da hukumar da ke shirya jarrabawar ta karyata makin da dalibar ta yi ikirarin samu a jarrabawar.

Ita dai hukumar JAMB ta ce dalibar ta samu maki 249, saɓanin maki 362 da take ikirarin samu, to sai dai a lokacin ɗalibar ta kafe cewa sakamakon da take ikirari shi ne na gaskiya.

Lamarin da ya sa gwamnan jihar Anambra Charles Soludo ya kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.

Kwamitin ya gayyaci ɗalibar da shugabar makarantar da kuma jami’an hukumar JAMB domin jin bahasin kowanne ɓangare.

Hukumar ta JAMB ta ce sakamakon da ɗalibar ke ikirarin samu wanda ke dauke da maki 362 sakamako ne na bagi, ba na gaskiya ba.

Haka kuma JAMB din ta bayyana yadda Ejikeme Mmesoma ta yi ta yunkurin neman samakamon jarrabawar tata a shafin hukumar cikin sa’o’i da dama, kuma a duk wadannan lokuta sakamako daya take samu daga hukumar wanda ke nuna cewa ta samau maki 249.

To sai dai Ejikeme Mmesoma ta shaida wa kwamitin cewa ta amince da wanna bayani da hukumar jami’an hukumar ta JAMB suka yi wa kwamitin.

Tana mai cewa da kanta ta kara makin sakamakon jarrabawar tata.

Ta ce ta yi amfani da wayarta wajen sauya sakamakon jarrabawar, kafin ta fitar da takardar sakamakon jarrabawar.

Kwamitin ya yi kokarin gano dalilin ɗalibar na aikata wannan laifi, to sai dai ta ce ba ta da wani kwakkwararn dalili.

Daga ƙarshe kwamitin ya bukaci ɗalibar ta gaggauta neman afuwa bisa wannan laifi da ta aikata, ta hanyar rubuta wasikar neman afuwa ga hukumar JAMB da hukumar Makarantar da ta kammala, sannan zuwa ga gwamnatin jihar Anambar.

Sannan kwamitin ya bukaci dalibar ta je a duba lafiyar kwakwalwarta, tare da yin kira da duka ɗaliban da ke rubuta jarrabawar da su tsaya inda dokokin hukumar ya iyakance musu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here