Tsohon shugaban majalisar wakilai, Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce babu wani sahihi ko madadin gwamnatin APC wajen ceto ’yan Najeriya.
Masari wanda tsohon gwamnan jihar Katsina ne, ya yi wannan jawabi a ranar Lahadi a garin Kafur, karamar hukumar Kafur a wajen kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomin jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga watan Fabrairu.
“Labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani cewa wasu ‘yan siyasa suna hada kai don hadewa waje daya ba komai ba ne illa tattara wadanda suka rasa tagomashin siyasa a cikin jam’iyyar APC, ta fuskar nade-nade ko na mukami.
Karin labari: Ko da ina gwamnatin APC ba zan ki fadar matsayata ba – Martani ga Bwala
“Kokarin da suka yi na kulla kawance ba zai kawar da hankalin jam’iyyar APC daga tunani da aiwatar da shirye-shiryen da za su iya rage radadin radadin talaka ba” inji tsohon Gwamnan Jihar Katsina.
Masari ya bukaci ‘yan Najeriya da su kara hakuri da gwamnatin APC, inda ya kara da cewa tabarbarewar tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta wani lamari ne da ya zama ruwan dare gama duniya.
Ya ci gaba da cewa a matsayinsa na guda cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC, zai ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da manufofin jam’iyyar.
Masari ya kara da cewa, “Ina APC yau, gobe da kuma ko da yaushe saboda bana cikin jam’iyyar don wani matsayi na siyasa ko nadi.”
Ya bukaci dukkan masu biyayya ga jam’iyyar APC da su yaɗa kyawawan ayyuka da manufofin jam’iyyar tare da rokon jama’a da su dauki duk wani gazawa a matsayin kuskuren dan Adam.
“Ina kira ga al’ummar karamar hukumar Kafur da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’arsu ga APC a zaben kananan hukumomi mai zuwa,” in ji Masari.