Rikicin Kakakin Majalisa: Anyi Arangama tsakanin Gbajabiamila da Wase.

Kakakin majalisar dokoki ta kasa Femi Gbajabiamila da mataimakinsa, Ahmed Idris Wase sun yi baram baram yayin zaman majalisar a ranar Laraba.

Kafin ya dage zaman majalisar, shugaban majalisar ya sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da ofishin dindindin na cibiyar horas da ‘yan majalisu da karfe 3:00 na yammacin ranar Alhamis.

Gbajabiamila wanda da farko ya yi watsi da Mataimakinsa, ya sake yin wata sanarwa kafin ya dawo ya yi masa jawabi yana mai cewa “Na dade a wannan majalisa na san cewa wannan shi ne karo na farko a tarihin wannan majalisa da mataimakin shugaban majalisar zai fito na fito ya nuna adawa da abin da Kakakin ya ce.

Amincewa da Hon. Tajudeen Abbas a matsayin shugaban majalisar wakilai ta 10 ya haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban majalisar da mataimakinsa.

An ce Wase ya ki halartar taron shugabanni da aka saba yi kafin zaman majalisar na yau da kullum, yayin da kuma ya kauracewa tattakin da kakakin majalisar ya yi zuwa zauren majalisar.

Ya fito karara ya zargi shugaban majalisar da marawa Tajudeen baya a matsayin shugaban majalisar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here