Kano: Ganduje Ya Gabatar Da Rahoton Mika Mulki Ga Abba Gida Gida.

Gwamnan jihar Kano mai barin gado Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da rahoton mika mulki na shekarar 2023 ga zababben gwamnan jihar, Engr. Abba Kabir Yusuf.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a wata ‘yar gajeriyar ganawa da aka yi a gidan gwamnatin Kano, Gwamna Ganduje wanda sakataren gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji ya wakilta ya jaddada kudirinsa na ganin an mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban Sakataren Yada Labarai na Zababben Gwamnan Jihar Kano ya fitar, ta ce Gwamna Ganduje ya bukaci gwamnati mai jiran gado da ta yi nazari kan rahoton mika mulkin tare da bayar da ra’ayin sa.

“A nasa jawabin, zababben gwamnan jihar Kano H.E.Abba Kabir Yusuf, wanda shugaban kwamitin mika mulki Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya wakilta ya nuna cewa kwamitinsa zai kai rahoto ga gwamna mai jiran gado tare da nazari kan sa” inji Sanarwar.

Sanarwar ta ce za a bai wa jama’a cikakkun bayanai game da bikin kaddamarwa bayan an cimma wasu yarjejeniyoyi tsakanin gwamnatoci masu barin gado da masu jiran gado.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here