An yi garkuwa da Matthew Abo, wanda shine kwamishinan yada labarai, al’adu, da yawon bude ido na jihar Benue, Hon.
An tattaro cewa an yi garkuwa da Abo a daren Lahadi, 24 ga Satumba, 2023, da misalin karfe 8 na dare, inda wasu ‘yan bindiga da suka kai hari gidansa da ke Zaki-Biam, karamar hukumar Ukum, (LGA), ta jihar.
An ce, masu garkuwa da mutanen da suka isa kan babura hudu, suka shiga gidansa tare da umurtar kowa da kowa, ciki har da matar kwamishinan da ‘ya’yansa, su kwanta.
Yayin da kowa ya bi umurninsu, sai suka tafi da shi a kan daya daga cikin babur.
An kuma tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun tilasta wa kwamishinan da bindiga ya zauna a bayan mahayin daya daga cikin baburan yayin da wani dan bindiga ya zauna a bayansa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hyacinth Alia, Kula Tersoo, ya ce “Eh an yi garkuwa da shi. Abin takaici, an yi garkuwa da shi a gidansa da ke karamar hukumar Ukum, da misalin karfe 8 na dare, Lahadi, 24 ga Satumba, 2023.