An Kama Matar Da Ake Zargi Da Kisan Kishiyarta Da Tabarya

022a0000 0aff 0242 e74e 08dad271efa4 w1023 r1 s
022a0000 0aff 0242 e74e 08dad271efa4 w1023 r1 s

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta cafke wata mata mai suna Maryam Ibrahim ‘yar shekara 20 bisa zargin ta kashe kishiyarta mai suna Hafsat Ibrahim ta hanyar kwada mata tabarya a kai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammad Wakili, ya bayyana hakan ne a wata tattunawa da yai da VOA.

Wakili ya ce a yammacin ranar Talata 29 ga watan Nuwamba aka kama matar da ake zargi da aika aikar a kauyen Gara na karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi.

A cewar kakakin, mijin matar mai suna Ibrahim Sambo dan shekara 40, a ranar 22 ga Nuwamba ya kai rahoton faruwar lamarin a hedikwatar ‘yan sanda ta Maina-maji.

Sambo ya fada wa ‘yan sanda cewa, a ranar Talata da misalin karfe 12:00 na rana, Maryam matarsa ta biyu, ta dauki tabarya ta shiga dakin uwargidanta Hafsat ‘yar shekara 32 ta kwada mata a kai.

Ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da matar wani asibiti inda likita ya ayyana cewa ta rasu.

A yayin da ake yi mata tambayoyi, Maryam ta amince da aikata laifin inda ta shaida cewa a ranar Talata, Hafsat (marigariyar) ta aiki danta Abdul’aziz Ibrahim dan shekara 5 da kunshin tsire ya ba ta. Bayan ta ci naman sai ta fara jin wani yanayi mara dadi har sai da ta kai ga yin amai.

Daga nan sai Maryam ta kira wata Fa’iza Hamisu ‘yar uwar maigidanta ta fada mata ainihin abin da ya faru, sai Fa’iza ta ce mata watakila ciwon gyambon ciki ke damunta har ta bata magani.

A karshe sai Maryam ta shiga kicin ta dauko tabarya ta nufi dakin uwargidanta da ke barci ta buga mata a kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here