Sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya fara aiki a babban ofishin hukumar da ke Abuja ranar Alhamis, inda ya bayyana naɗin nasa a matsayin kira daga Allah domin hidima ga ƙasa.
Amupitan, wanda shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya rantsar a fadarsa, ya karɓi ragamar hukumar daga May Agbamuche-Mbu, wadda ta riƙe matsayin shugaban riko tun bayan barin Farfesa Mahmood Yakubu.
Yayin ganawa da manyan daraktocin hukumar bayan karɓar aiki, Farfesa Amupitan ya yi alkawarin gudanar da aiki bisa gaskiya, amana da tsari, yana mai cewa manufarsa ita ce tabbatar da ingantaccen tsarin zaɓe a Najeriya.
Ya ce babu wurin sassauci wajen kare sahihancin zaɓe, domin wajibi ne a tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa yana da tabbacin cewa ƙurarsa ta ƙididdige. Ya kuma tabbatar da cewa kulawa da jin daɗin ma’aikata da inganta yanayin aiki zai kasance a sahun gaba a lokacin jagorancinsa.
Labari mai alaƙa: Tinubu ya rantsar da Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar Zabɓe ta ƙasa
Farfesa Amupitan ya bayyana zaɓen gwamna na Anambra da ke tafe a matsayin gwaji na farko da hukumar za ta fuskanta, inda ya ce za a yi ƙoƙari wajen tabbatar da gaskiya da amana a cikin tsarin gudanarwa.
Ya gode wa May Agbamuche-Mbu bisa irin rawar da ta taka a lokacin rikon hukumar, tare da yabawa ma’aikatan hukumar saboda jajircewarsu wajen ciyar da hukumar gaba.
Hukumar INEC karkashin sabon shugaban ta sha alwashin tabbatar da gudanar da sahihan zaɓe da zai karfafa amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar.













































