Wani mummunan lamari ya auku a unguwar Hotoro da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, bayan wani ya kashe Ladani mai kiran salla jim kadan bayan ya kira sallar asuba a masallaci.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a masallacin Yusuf Garko da ke unguwar Maraba, inda aka kai hari kan Ladan Malam Zubairu, mazaunin yankin, aka kuma yanka shi da wuka daga hannun wani da ba a tantance ba.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ihun neman taimakon da mamacin ya yi ya sanar da mazauna yankin, wanda hakan ya sa suka fito tare da bin sawun wanda ake zargi.
An kama wanda ake zargin daga bisani bayan tara-tara da taron jama’a suka yi, inda aka kashe shi a wurin kafin isowar jami’an tsaro.
Taron jama’ar ya kuma kona gidan wanda ake zargi, lamarin da ya janyo lalacewar dukiya tare da kara tayar da hankula a unguwar.
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa an shawo kan lamarin gaba daya, kuma an maido da zaman lafiya.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an dauki gawarwakin mamacin da wanda ake zargi zuwa asibitin koyarwa na Mohammed Abdullahi Wase, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu, tare da kiran jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro.













































